Pages

Friday 18 October 2019

El Clasico: An daga wasan Barcelona da Real Madrid saboda fargabar rikici

An dage wasan hamayya na El Clasico na wannan watan tsakanin Barcelona da Real Madrid saboda tsoron rikicin neman 'yancin Kataloniya.


Tun da fari an shirya yin wasan ne ranar 26 ga watan Oktoba, amma an shafe kwanaki ana rikici a Barcelona bayan da aka kulle wasu 'yan awaren Kataloniya tara ranar Litinin.

Daga Barcelona har Real Madrid ba su amince da kiran da ake yi na mayar da wasan birnin Madrid ba.

Duk kungiyoyin biyu za su gana ranar Litinin don saka sabuwar rana.

Koci Ernesto Valverde ya ce Barcelona ba ta yarda da mayar da wasan birnin Madrid ba saboda wasan da za su yi da Slavia Prague a Gasar Zakarun Turai ranar 23 ga watan Oktoba, kwana uku kafin ranar da aka sa don yin wasan El Clasico din.

La Liga ta nemi a daga wasan ne saboda abin da ta kira "abin da ka iya faruwa wanda ya fi karfinmu" yayin da ake sa ran yin wasu jerin zanga-zanga a Barcelona a ranar wasan.

An shiga kwana na biyar ana rikici a yankin Kataloniya na Spaniya inda masu zanga-zanga ke fada da 'yan sanda.

Dubun-dubatar mutane ne ke daga tutar neman 'yancin kai da ke ihun "a bai wa fursunonin siyasa 'yanci" suka yi maci a fadin yankin Kataloniya ranar Juma'a.

A kalla mutum 96 ne suka ji rauni a fadin yankin.

Kataloniya wani yanki ne mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a arewa maso gabashin Spaniya.

A wata kuri'ar raba gardama da aka kada ranar 1 ga watan Oktoban 2017 - Kotun Kundin Tsarin Mulki ta Spaniya ta ayyana ta a matsayin haramtacciya, kusan kashi 90% na 'yan Kataloniya ne suka kada kuri'ar goyon bayan samun 'yancin kan. Sai dai yawan wadanda suka kada kuri'ar kashi 43% ne kawai.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment