Pages

Sunday 8 December 2019

Abinda akewa Sowore zai iya shafar Dangantakar Kasar Amurka da Najeriya>>Inji Sanatn kasar Amurka

Wani sanatan kasar Amurka, Robert Menendez wanda kuma yana cikin kwamitin kula da huldar kasashen waje na kasar ya bayyana cewa yanayin yanda Najeriya ke wa Sowore da sauran 'yan Jarida zai iya shafar dangantakar Amurkar da Najeriya.



Sanatan ya bayyana hakane a ganawar da yayi da 'yan Jarida akan kamun da jami'an DSS sukawa Sowore inda yace sau 2 kotun Najeriya ke bada umarnin sakinshi amma DSS na yin watsi da umarnin.

Yace anawa Sowore wanda mijine kuma uba ga mutanen da 'yan asalin kasar Amurkane, wannan abu kawai dan yace zai yi abinda 'yancinshi ya bashi damar yi kuma hakan na faruwane a kasar da ake Dimokradiyya.

Sanatan yace abinda akewa Sowore Amurka na gani kuma Duniya ma tana gani, yace dan jarida wanda ke saka rayuwarshi cikin hadari dan nemo gaskiya kamata yayi a rika karramashi ba wai kullewa ba.

Yace yayi magana da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya dan yaji abinda Amurka ke yi kan lamarin na Sowore sannan kuma zai ci gaba da tuntubar hukumomin Amurkar dan ganin an sake duba dangantakar Najeriya da Amurkar kan wannan lamari.






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment