Pages

Sunday 8 December 2019

Watanni 3 dana kwashe ina Casu ne suka sa Anthony Joshua yayi nasara akaina>>Inji Andy Ruiz

Bayan shan kashi da yayi a hannun Anthony Joshua, Andy Ruiz ya bayyana cewa, casun da yayi ta yi na kusan tsawon watanni 3 ne yasa yayi rashin nasara a fadan da suka yi a daren jiya.




Ruiz ya bayyanawa 'yan Jarida cewa bai fara Atisayen shiryawa wasan da wuri ba.

Da aka tambayeshi shin da zasu sake fada da Joshua me zai canja ko kuma wane irin shiri zai yi? Sai ya bayyana cewa zai saurari abinda me horas dashi ya gaya mai da kuma abinda mahaifinshi ke gayamai.

Yace me horas dashi ya so ya fara Atisaye a watan Yuni amma sai yake tunanin zai iya fara atisaye  shi kadai ba tare sa an horar dashi ba, sai a watan Satumba ne ya fara Atisaye da me horas dashi.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment