Pages

Wednesday 26 June 2019

Karka yi murna tukuna, kotu bata hanani duba rumbun INEC ba

Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar yacewa shugaba Buhari ya daina murna tukuna wai dan ya ji an ce kotu ta hanashi leka rumbun tattara sakamakon zaben ta.



Atiku ta hannun me bashi shawara akan kafafen watsa labarai, Paul Ibe ya bayyana cewa asalima ba hanashi duba rumbun tatara sakamakon INEC kotu ta yi ba, tacene ba'a zo kan wannan ba tukuna a shara'ar da ake har yanzu ana farko-farkon shari'arne, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Atikun ya ci gaba da cewa ta yaya za'a ce babu rumbun tattara sakamakon bayan da kafafen watsa labarai da yawa sun yi hira da ma'aikatan INEC kuma sun tabbatar musu cewa da akwai, sannan ita kanta gwamnatin ta ware kudin kula da rumbun tattara sakamakon a kasafin kudin 2019?

No comments:

Post a Comment